Abin
mamaki baya karewa a cikin Duniyar nan tamu, wani matashi mai suna
Frank Joseph ya fada cikin wani ibtila'i bayan ya gagara saukar da wani
buhun massara da ya sata a gidan wata tsohuwa a Nyambwiro. Wannan lamari
ya faru a Mbezi a Dar'es Salam na kasar Tanzania.
Frank
dan shekara 23 ya kai kanshi caji ofis na 'yansanda bayan buhun da ya
sata na massara mai nauyin kilo 20 ya makale a kanshi.
Wannan
matashi ya yi iya kokarin da zai yi tare da neman taimako da ya wajaba
domin a taimaka wannan buhu ya rabu da shi amma lamarin ya gagara.
Sakamakon haka Frank ya kai kanshi ga 'yansanda domin su cece shi.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari