Wani
bahaushe mai aikin okada ya gamu da iftila'i bayan kwayoyin tramal da
ya hadiye suka narke sakamakon haka kansa ya juye ya fado daga babur da
yake tukawa a jihar Delta.
Rahotanni sun ce shi dai
wannana dan okada ya dauko wasu 'yan mata ne guda biyu, kuma yana cikin
tafiya ne sai suka ga ya yi burki kuma ya fadi nan take.
Jama'a
da ke wajen sun matse bakinsa suka dura masa suga bayan dan okadan ya
yi ta kokarin yin fada da mutane.Daga bisani kuma aka samo bokitin ruwa
aka yi ta kwara masa kafin ya farfado.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari