• Labaran yau


  An sa dokar ta baci a Kaduna, kowa ya zauna a gida

  Rahotun Legit Hausa

  Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar ta baci a fadin jihar saboda mutane sun sabawa dokokin farko da gwamnatin ta sanya domin hana shigowa da yaduwar cutar Coronavirus jihar. Mataimakiyar gwamnan, Hadiza Balarabe, wacce ta sanar da hakan ranar Alhamis ta ce wannan shawara da aka yanke ya yi muwafaqa da kudin tsarin mulkin Najeriya.

  A cewarta, kwamiti na musamman kan yakar cutar ta gana domin tattauna yadda cutar ke cin rayuka sauran jihohi da kasashen waje. Tace: "Kwamitin ta samu rahoton cewa mutane sun sabawa dokokin hana taro a sanarwa daban-daban da tayi cikin kwanaki bakwai da suka wuce."

   "An samu rahotonnin mutane sun yi ko oho da dokar hana hawa babur, Keken 'a daidaita sahu' , da motoci fiye da fasinjoji biyu a kujera da aka sanya." "Saboda haka, daga daren Alhamis, 26 ga Maris 2020, wajibi ne dukkan mazauna jihar Kaduna su zauna a gida . Babu zuwa aiki, babu kasuwanci, babu zuwa wuraren ibada."

  "Mutanen da aka amincewa fitowa kadai sune jami'an kwana-kwana, jami'an kiwon lafiya da jami'an tsaro." "Za'a kulle Masallatai da cocuna, babu Sallar Jami'in da za'a amince a gudanar ciki ko waje." "Duk wajen Ibada ko taron da aka kama ana taro, lallai sun saba doka kuma za'a iya kwace takardan mallakan filin wajen ko kuma kwace wajen."

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An sa dokar ta baci a Kaduna, kowa ya zauna a gida Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama