Ina jima'i da 4 dag cikin matana a kullum, Magidanci mai mata 28 da 'ya'ya 111

Wani bawan Allah dan kasar Zimbabwe mai suna Shadreck Chimbare ya ba mutane mamaki bayan ya gaya wa Duniya cewa yana da mata 28 da yaya 111 yayin da yake zantawa da jaridar Mirror na kasar Zimbabwe.

Tsohon dan yakin kwatar yanci daga turawan mulkin mallaka a kasar ta Zimbabwe, Shadreck Chimbare ya ce yana yin jima'i da 4 daga cikin matansa 28 a kowane rana, kenan yakan sadu da dukkannin matansa akalla sau daya a kowane mako.

Shadreck Chimbare ya ce yana gane dukkannin yayansa tare da sunayensu ba tare da uwayensu sun taimaka masa wajen gane yayansa ba tare da sunayensu. Ya kuma kara da cewa, 58 daga cikin yayansa maza ne kuma babba daga cikinsu shi ne mai shekara 26, wanda ke cikin rundunar sojin kasar Zimbabwe, kuma shi ma dansa yana da mata 3 a halin yanzu.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika  
Saratu ta warke cutar olsa (ulcer) da ta yi fama da shi, karanta ababe da ta hada ta sha 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post