Gwamnatin Kebbi za ta kawo dokar haramta barace-barace a kan titi

Rahotun Legit Hausa

Gwamnatin jihar Kebbi ta na yunkurin haramta barace-barace a kan titi da ake fama da shi. Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a Yau Ranar Litinin. Rahoton da mu ka samu ya bayyana cewa gwamnatin Atiku Abubakar Bagudu za ta duba yiwuwar kafa dokar da za ta haramta bara a kan titunan jihar Kebbi.

Mai girma gwamna Atiku Abubakar Bagudu ya bayyana wannan da kansa a wajen wani taro da kungiyar Daliban da ke karantar ilmin shari’a su ka shirya a jiya. Wannan kungiya ta NUKELS ta Daliban jihar Kebbi da ke karatun ilmin shari’a ta yi taron ta na farko ne jiya a Garin Birnin Kebbi, inda ta gayyaci Gwamnan.

Sanata Atiku Abubakar Bagudu ya ce gwamnatinsa za ta kafa dokar da za ta hana bara, wannan doka za ta ba gwamnati damar cafke iyayen yaran da ke bara. Idan har an kirkiro wannan doka kuma an sa mata hannu, gwamnatin Kebbi za ta samu hurumin damke Iyaye da masu kula da Yaran da aka bari su na bara.

Kebbi ta bi sahun gwamnatin jihar Kano inda mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya haramta bara da niyyar koyawa Almajirai ilmin boko na zamani. Gwamnatin Atiku Bagudu za ta tabbatar kowane Mahaifi ko mai riko ya kula da ‘Ya ‘yansa.

Wannan zai bada damar a rika lura da ‘Ya ‘ya da kyau a jihar Kebbi. A wajen wannan taro na ‘Daliban shari’an Kebbi, Ministan shari’an Najeriya, Abubakar Malami SAN, ya yi jawabi a matsayinsa na babban Lauya daga jihar ta Kebbi.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika  
Saratu ta warke cutar olsa (ulcer) da ta yi fama da shi, karanta ababe da ta hada ta sha 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN