Gwamnatin jahar Katsina ta dakatar da Sallar Juma’a da bautan Kiristoci

Rahotun Legit Hausa

Gwamnatin jahar Katsina ta sanar da daukan matakin dakatar da sallar Juma’a tare da tarukan bautan mabiya addinin kirista a coci coci, a wani mataki na kandagarki domin kauce ma yaduwar annobar cutar nan mai toshe numfashin dan Adam, Coronavirus.

Kwamishinan watsa labaru na jahar, Abdulkarim Sirikam ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya raba ma manema labaru a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris inda yace duk wani taron daurin aure ko na siyasa sun haramta a wannan lokaci.

Don haka yace gwamnati na shawartar jama’a su takaita ire iren tarukan nan kamar yadda hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC, ta umarta duba da yadda cutar Coonavirus ke cigaba da yaduwa a kasar. “Haka zalika gwamnati na kira ga jama’a su yi biyayya ga wannan sabon umarni, sa’annan su cigaba da yi ma kasa addua game da wannan mugunyar jarabawa da duniya ke fama da ita.” Inji kwamishina Abdulkarim.

A wani labari makamancin wannan kuma, rundunar Yansandan jahar Katsina ta dauki alwashin tabbatar da dabbaka umarnin gwamnatin jahar na hana sallar juma’a da duk wasu sauran taruka a jahar, kamar yadda babban sufetan Yansandan Najeriya ya bata umarni.

Kakakin Yansandan jahar, SP Gambo Isah ne ya bayyana haka inda yace dole ne masu shaguna da kamfanoni su samar da sinadarin wanke hannu mai kashe kwayoyin cututtuka, watau Hand Sanitizer ga abokan huldarsu.

Haka nan ya wajaba su samar da na’urar gwajin zafin jikin dan Adam a wuraren ayyukansu, bugu da ya nanata bukatar gwamnati na ganin jama’a sun takaita zirga zirgarsu, daga karshe kuma ya yi kira ga DPO na kowanne yanki su saki duk mutumin da laifinsa bai wuce a bada belinsa ba. A wani labari kuma,

A kokarinsa na hada kai domin ganin an ci galaba a kan annobar Coronavirus mai toshe numfashin dan Adam, shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Isiyaka Rabiu ya sanar da kyautar naira biliyan 1 ga gwamnatin tarayya. Haka zalika, baya ga tallafin tsabar kudi N1,000,000,000 a yanzu haka Abdul Samad ya yi odan karin kayan asibiti da kuma hada da na’urori, injina da kayan gwajin cutar Coronavirus da za’a yi amfani dasu a jahohi guda 9.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN