COVID-19: FG ta bada umarnin sakin 70% na 'yan gidan gyaran hali

Rahotun Legit Hausa

Matakan hana yaduwar muguwar cutar coronavirus da gwamnatin tarayya ke dauka a kasar nan suna da yawa ,kuma a halin yanzu har sun kai gidajen gyaran hali. A cikin wannan kokarin ne gwamnati ta bada umarnin cewa a saki wadanda ake kan shari'arsu amma ake garkame dasu a gidajen.

Kamar yadda ministan lamurran cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayyana, an yi hakan ne don hana yaduwar cutar a gidajen gyaran hali. Aregbesola ya bada wannan umarnin ne a yayin wani taron gaggawa da ya kira a ofishinsa a Abuja a kan yadda za a hana yaduwar cutar a gidajen gyaran hali. Bayan taron ne ministan ya fitar da takarda wacce aka mika ga manema labarai ta hannun daraktan yada labarai da hulda da jama'a,

Mohammed Manga, inda ya ce wannan umarnin ya biyo bayan hukuncin kwamitin fadar shugaban kasa na yakar cutar ne. Ya kara da cewa an dauka matakan ne don kare masu zama a gidajen gyaran halin, ma'aikatansu da kuma sauran 'yan Najeriya. Aregbesola, wanda ya jaddada cewa kasar nan tana cikin mawuyacin hali wanda ke bukatar hadin kai kowa don tabbatar da cewa cutar ba ta yadu ba, ya ce ba za su zuba wa gidajen gyaran halin ido ba.

Ya yi kira ga Antoni Janar kuma ministan shari'ar kasar nan, manyan alkalan jihohi, gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren shari'a da su dauka matakan gaggawa don tabbatar da cewa an rage yawan jama'ar da ke dankare a gidajen gyaran halin kasar nan. Kamar yadda yace, yawan wadanda ke cikin gidajen gyaran halin sun yi yawa kuma duba da halin da kasar nan ke ciki, akwai yuwuwar in cutar ta shiga tayi barna.

Ya kara da cewa akwai jama'a da yawa da ke gidan amma suna jiran kammalar shari'arsu, wadanda sune suka kunshi kashi 70 na wadanda ke gidan. Ya yi kiran gaggawa a kan hakan tare da bukatar a kawo hanyar da za a shawo kan wannan kalubalen.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN