Rahotun Jaridar Aminiya
Da safiyar ranar Lahadi ne al’ummar unguwar Abule Ado da ke
yankin Festak a karamar hukumar Amuwo Odofin a jihar Legas, suka wayi
gari da karar fashewar wasu abubuwa wadanda suka yi sanadiyyar tashin
gobarar da tayi salwantar rayuka da dama da kuma kone tare da lalata
akalla gidaje 50 a yankin.
Wasu mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa, gobarar ta samo asali
ne bayan da wata motar tifa da ke sauke kasa a yankin ta kama da wuta,
inda nan take wutar ta yadu zuwa sassan da bututun man fetur ke shinfide
a karkashin kasa.
Kana zuwa yanzu jami’an kashe gobara ta gwamnatin jihar Legas da na
tarayya sun yi kokarin kashe wutar, haka zalika jami’an hukumar bada
agajin gaggawa ta kasa wato NEMA a takaice sun isa wajen domin bada
agaji.
Babban jami’in hukumar da ke kula da shiyyar jihohin Kudu maso Yamma
Ibrahim Farinloye, ya shaida cewa wutar ta tashi ne daga inda bututun
man fetur din suke, ya ce an girke manyan motocin kashe gobara 3 da suke
aikin kashe wutar kana zuwa yanzu ba za a iya sanin adadin mutanen da
suka hallaka sakamakon gobarar ba, sai dai gidaje akalla 50 sun salwanta
a sakamakon ibtila’in.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari