'Yan boko haram 2 sun yi saranda, sun tona asirin wadanda suke yi wa aiki

Rahotun Legit Hausa

Mun samu labari cewa Dakarun Sojojin kasan Najeriya na Operation Lafiya Dole sun lallasa ‘Yan ta’addan Boko Haram da su ka fitini Yammacin Afrika da bagarorin Najeriya. Babban Jami’in Sojan da ke lura da sha’anin yada labarai a Najeriya, Kanal Aminu Ilyasu, ya fitar da wani jawabi a Ranar Lahadi, ya na bayyana irin nasarar da Soji su ka samu.

Kanal Aminu Ilyasu ya shaidawa Jama’a cewa Rundunar Sojojin kasar sun aukawa ‘Yan ta’addan Boko Haram a Garuruwan Damboa da Garkida da ke Borno da kuma Adamawa. Aminu Ilyasu ya ke cewa an yi wa ‘Yan Boko Haram lahani da wannan hari da aka kai masu a ‘yan kwanakin nan. Ana sa ran hakan zai taimaka wajen kassara ‘Yan ta’addan.

Da ya ke bayani, Jami’in sojan ya bayyana cewa wasu daga cikin ‘Yan ta’addan na Boko Haram sun mika wuya ga Dakarun Najeriya. Jaridar Daily Trust ta bayyana mana wannan. Ilyasu ya bada sunayen wadanda su ka mika kansu da kansu ga Dakarun Bataliya ta 202 da: Musa Mohammed da Maina Liman wadanda su ke da shekara 21 da kuma 35 a Duniya. Wadannan ‘Yan ta’adda sun mika wuya ne a Ranar 5 ga Watan Maris.

‘Yan ta’addan sun kuma bayyana cewa su na yi wa wani babban Sojan Boko Haram mai suna Nakib aiki. Nakib wanda ya kai matsayin Kyaftin a cikin Rundunar ‘Yan ta’addan ya na zaune ne a wani Kauye mai suna Bula Umar kamar yadda Liman da Mohammed su ka bayyana.

Bayan sun shiga hannun Jami’an tsaro, Mohammed da Liman sun bayyana cewa Sojojin Najeriya sun kashe Mayakan Boko Haram da-dama a hare-haren da su ka kai kwanaki. Rundunar Sojin Najeriya ta shaidawa hukumar dillacin labarai cewa wannan ya nuna akwai Mayakan Boko Haram rututu da ke neman mika wuya domin sun gaji da yakin.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN