Ga jerin sunayen kasashen Duniya guda 16 da cutar coronavirus bata bulla ba kawo yanzu

Rahotun Legit Hausa

Duk da cewa cibiyar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cutar coronavirus a matsayin annoba wacce babu inda aka tsira daga sharrinta, akwai wasu kasashen duniya kadan da har yanzu cutar bata bulla ba.

Bayan fara sanin cutar da aka yi a Wuhan a watan Disamba na shekarar da ta gabata, an tabbatar da ta kama mutane a kalla 788,000 a fadin duniya tare da halaka a kalla 38,000. Amma kuma, akwai kasashe 16 da har yanzu babu cutar ko alamarta.

A Afrikac, kasashe irin su Lesotho, Sudan ta Kudu, Yemen, Sierra Leone, Burundi da Malawi da ke Yammacin Sahara, har yanzu babu wanda ya kamu da cutar. A nahiyar Asia, kasashe irinsu Turkmenistan, Tajikistan da Korea ta Arewa duk babu labarin bullar cutar.

Akwai wasu kasashen da ke tsibirin Pacific wadanda aka sani da wuraren shakatawa, har yanzu ba a samu bullar cutar ba saboda a kebance suke da kuma rashin ci gabansu, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito

Wadannan yankunan sun hada da Tonga, Samoa, Vanuatu, tsibirin Cook, Niue da Tuvalu. Cu tar coronavirus ta yadu a kasashe a kalla 178 da kuma yankuna da dama na fadin duniya. A duk kasashen, a kalla mutane 166,700 ne da aka samu da cutar suka warke garas.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN