An bizine wani mutum mai shekara 74 ranar Asabar bayan an saka gawarsa a cikin mota kuma aka saka motar a cikin kabarinsa marmakin akwatin gawa a gabacin Cape da ke kasar Afrika ta kudu.
Mun samo cewa shekaru biyu da suka gabata ne Tshekedi Pitso, ya shaida wa iyalinsa cewa idan ya mutu, yana son a bizine shi a cikin motarsa kirar Mercedes Benz.
Jama'an garin Jozanashoek da ke Sterkspruit a gabacin Cape sun kasance a cikin mamaki, domin an saka gawar Tshekedi Pitso a cikin motarsa, daga bisani aka saka motar tare da gawar a cikin kabari. Tshekedi Pitso basarake ne a wannan garin, kuma jigo a jam'iyar UDM.
Kafin mutuwarsa, Tshekedi Pitso ya mallaki motoci kirar Mercedes Benz da dama, amma ya fi son wacce ya saye daga baya kirar 1980s
E500, wacce a cikinta ne aka saka gawarsa aka binne shi.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari