RASHIN TAIMAKO GA WADANDA BASU AIKIN GWAMNATI
Kawo yanzu a jihar Kebbi rashin tallafi zai iya jefa wadanda suka dogara da yin aikin hannu a kullum, lebarori, kanikawa da saura ire iren wadannan jama'a cikin kuncin rayuwa.
RUFE MAKARANTUN ISLAMIYYA
Rufe makarantun addinin Musulunci gaba daya da gwamnati ta yi, masana sun bukaci da gwamnati amfani ta yi da Malaman makarantun ta hanyar basu sadaka mai kauri domin gudanar da addu'oi domin neman yardar Allah wajen kawo sauki da karshen wannan annoba.
Gwamnatin jihar Kebbi ta bayar da miliyoyin domin bukukuwan al'ada na Regatta, kamun kifin na Argungu Fishing Festival, yanzu lokaci ya yi da Gwamnati ya kamata ta fitar da miliyoyin jama'a domin ba Malamai domin su yi addu'an neman Allah ya kowo saukin annobar.
RASHIN KYAKKYAWAR TSARIN TALLAFI
Kawo yanzu, babu wabi bayyanannen tsari da gwamnatin jihar Kebbi ta sanar na aniyarta na tallafawa jama'a da aka bukaci su zauna a gida da wasu kayakin masarufi. Yanzu haka a cikin garin Birnin kebbi, a unguwar Nassarawa 2, ana sayar da jakar ruwa na piyawata a naira dari da ashirin marmakin naira sittin a baya. Wannan ya faru ne tsakanin ranar Alhamis zuwa Asabar. Da kyar ake samun ruwan a wasu shaguna.
Jama'an jihar Kebbi sun yi kira ga gwamnatin jihar Kebbi, da ta yi koyi da takwaranta gwamnan jihar Lagos wajen kai kayakin masarufi, abinci, ruwan sha da sauran ababen amfani da su domin kariya ga jama'a a gidajensu.
SHARHI
A daidai wannan lokaci,wajibi ne Gwamna Atiku Abubakar Bagudu ya saurari masu bashi shawara, wajibi ne masu ba Gwamna shawara su yi aikinsu bisa gaskiya da amana. Binciken mu tare da sakamakon jin ra'ayin jama'a a garin Birnin kebbi da kewaye ya nuna cewa, jama'a na bukatar agaji dangane da wannan umarni na zama a gida.
Idan ka hana mutum fita ya nemi abici da abin sha domin rufin asirin iyalinsa, kamata ya yi a sama masa tallafi domin ta haka zai ji dadin yin biyayya cikin sauki ga umarni.
Rahotun Isyaku Garba Zuru
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari