Duba Jerin jihohin Najeriya 7 da aka tabbatar da bullar kwayar cutar coronavirus

Rahotun Legit Hausa

Tun farkon samun bullar kwayar cutar coronavirus a Najeriya ta hannun wannan dan kasar Italiya, an tabbatar da samun kwayar cutar a jihohin Najeriya 7. Ya zuwa yanzu kwayar cutar coronavirus ta hallaka mutane 15,000 a fadin duniya.

Mutum daya ne ya mutu a Najeriya bayan kamuwa da kwayar cutar coronavirus, amma adadin masu dauke da cutar ya kai mutum 46, kamar yadda kididdiga da aka yi da safiyar ranar Laraba, 25 ga watan Maris, ta nuna.

Ga jerin jihohin Najeriya da aka tabbatar da samun kwayar cutar coronavirus da adadin mutanen da suka kamu da ita;

Jihar Legas - mutum 30, Abuja - mutum 8, Ogun - mutum 3, Ekiti - mutum 1, Edo - mutum 1, Bauchi - mutum 1, Edo - mutum 1.

 Tuni jihar Legas, da ke da mafi yawan wadanda suka kamu da kwayar cutar, ta bayar da umarnin kasuwannni, ana sa ran rufe kasuwannin ne daga ranar Alhamis. Yawacin mutanen da aka samu da kwayar cutar corona, 'yan Najeriya ne da suka dawo daga kasashen ketare, musamman turai.

An tabbatar da samun kwayar cutar a jikin manyan jami'an gwamnati guda uku.Shugaban ma'aikatan farar shugaban kasa, Abba Kyari, shine na farko da aka fara samu dauke da kwayar cutar.

Na biyu shine gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, sai kuma kakakin majalisar jihar Edo.Ya zuwa yanzu, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da wasu gwamnoni da manyan jami'an gwamnati sun killace kansu bayan sun gano cewa sun yi mu'amala da masu dauke da kwayar cutar.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN