• Labaran yau


  Atiku ya yi alkawarin bada gudunmuwar N50m domin matsayin tallafi ga yan Najeriya

  Rahotun Legit Hausa

  Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin bada gudunmuwar milyan hamsin cikin kudin tallafin da ake shirin baiwa yan Najeriya domin saukake radadin zaman gida sakamakon cutar Coronavirus.

  Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Laraba. Ya ce zai bada gudunmuwar ne ta kamfaninsa Priam Group inda har gwamnatin tarayya ta shirya samar da tallafi ga yan Najeriya.

  Yace: “Ina jinjinawa dukkan mutane da kamfanonin da suka taimakawa yan Najeriya yayin wannan annoba. Ina kara kira ga wasu kamfanonin da masu hannu da shuni su taimakawa mutane a irin wannan lokaci.“

  “Priam Group ta yi alkawarin N50 million a madadina matsayin gudunmuwar tallafin da ya za a yiwa yan Najeriya.“ Za ku tuna cewa daya daga cikin yaran Atiku Abubakar ya kamu da cutar kuma ana jinyarsa a asibitin koyarwan jamiar Abuja dake Gwagwalada.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

  Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Atiku ya yi alkawarin bada gudunmuwar N50m domin matsayin tallafi ga yan Najeriya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama