Duba hukunci da Kotu ta yi wa kwarto da ya shiga gidan matar aure sanye da hijabi a Kebbi

Kotun shari'a da ke Nassarawa 1 Birnin kebbi, ta yanke wa Abubakar Garba hukuncin bulala hamsin (50) tare da daurin shekara daya (1) a Kurkuku, sakamakon kama shi da laifin shiga gidan mutane da niyyar aikata zina da matar aure.

Idan baku manta ba, Mujallar ISYAKU.COM ya kawo mako labarin yadda Abubakar ya saka Hijabin mata, ya shiga gidan Aliyu Hakimi da ke kauyen Asarara ranar 3/3/2020, da niyyar aikata zina da matar aure a cikin gidan, kafin Allah ya tona asirinsa.

An zartar wa Abubakar da bulala hamsin bisa umarnin Kotu, daga bisani aka tasa keyarsa zuwa Kurkuku, domin zaman gyara hali har shekara daya, kamar yadda doka ta tanada.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN