Rahotun Jaridar Aminiya
Yayin da cutar coronavirus ke ci gaba da yaduwa a kasashe
daban-daban, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta fitar da wani rahoto
wanda ta kwatanta siffofin cutar da mura.
A cewar WHO, ko da yake cututtuka biyu na kama kafar numfashin
dan-Adam, akwai muhimman bambance-bambance a tsakaninsu da kuma yadda
suke yaduwa.
Inda suka yi kama
Duka cututtukan biyu na yaduwa ne ta hanyar taba mai dauke da su.
Akwai tabbacin idan ka taba wani mutum ko wani abu mai cutar a jikinsa
sannan ka taba fuskarka za ka kamu. (Akwai kuma yiwuwar cutar
coronavirus na yaduwa ta hanyar feshin majina ko yawu da mai ita ya yi
wadanda ka iya yawo a iska.)
Alamun kamuwa da su da dama sun yi kama da juna: Duka cututtukan biyu
na kai hari ne a kan kafar numfashi ta hanyoyi daban-daban. Dukkaninsu
suna haddasa zazzabi, da gajiya ko kasala, da tari. Idan lalurar kafar
numfashi ta yi tsanani tana iya zama cutar numoniya (pneumonia) wacce ka iya kisa.
Bambance-bambance guda shida
— Ga alama cutar coronavirus ba ta kai mura saurin yaduwa ba.
Mai yiwuwa wannan ne bambanci mafi girma a tsakanin cututtukan biyu:
Alamun mura sun fi saurin bayyana a jikin wanda ya kamu, kuma alamunta
sun fi saurin bayyana mutum a tsakanin wanda ya kamu da wanda ya yada
masa.
A cewar WHO, lokacin da ake dauka tsakanin bayyanar alamun cutar
coronavirus a jikin mai ita da wanda ya yadawa kwana biyar ne yayin da
lokacin da alamun mura kan bayyana a tsakanin mai ita da wanda aka
yadawa ya haura kwana uku. Saboda haka mura ta fi saurin yaduwa.
— Watsi (da kwayoyin cuta): Wannan shi ne abin
da ke faruwa idan kwayar cuta ta kama mutum, ta hayayyafa, sannan ta
fara watsuwa. Wannan ke sa mai ita ya yada ta ga wasu. Wasu mutane kan
fara yada cutar coronavirus kwana biyu bayan sun kamu, tun ma kafin su
fara nuna alamun kamuwa, ko da yake a cewar WHO ba wannan ce hanyar da
ta fi yaduwa ba.
Ita kuwa mura, bisa al’ada ana fara yada ta ne kwana
biyu bayan alamunta sun bayyana a kuma ci gaba da hakan har mako guda.
Sai dai kuma sakamakon wani nazari da mujallar The Lancet ta
wallafa a wannan makon ya nuna cewa wadanda suka warke sun ci gaba da
yada cutar coronavirus har tsawon kwana 20 ko har lokacin mutuwarsu.
Wannan ya nuna cewa masu dauke da cutar Coronavirus sun fi dadewa suna
yada ta a kan masu mura.
— Ana kukan targade…. Galibi, cutar Coronavirus
kan haddasa wasu cuttukan akalla biyu. Wani lokaci mura kan haddasa wata
cutar, misali numoniya, amma abu ne mai wahala mai mura ya kamu da wasu
cututtukan har biyu. Sai dai WHO ta yi gargadin cewa yanayi na da
muhimmanci (misali ta yiwu wanda ya kamu da cutar Coronavirus da ma yana
da wata larurar).
— Manya ne ke yada Coronavirus. Yayin da yara ne
galibi suke yada kwayoyin cutar mura, alamu na nuna cewa cutar
Coronavirus ta fi yaduwa a tsakanin manya. Hakan kuma na nufin cewa
manya ne—musamman wadanda suka manyanta suke da wata larura—suka fi
kamuwa da ita.
A cewar jaridar Washington Post, kwararru na mamakin dalilin
da ya sa yara ba su cika kamuwa da Coronavirus ba.
Wasu na hasashen
cewa suna da wata kariya ne da suka samu daga wasu nau’ukan coronavirus
da ke cikin kwayoyin cutar mura, yayin da wasu kuma ke cewa a koda
yaushe halittun garkuwar jikin yara a fadake take don haka ta fi ta
manya kuzari wajen yakar COVID-19.
— Cutar Coronavirus ta fi kisa. Zuwa yanzu yawan
mutuwa sakamakon cutar Coronavirus ya kai kashi uku zuwa hudu cikin
dari na wadanda suka kamu, ko da yake akwai yiwuwar ya kasance kasa da
haka saboda akwai wadanda suka kamu da dama da ba a ba da rahotonsu ba.
Yawan masu mutuwa sakamakon mura kuwa kashi 0.1 ne cikin dari na masu
kamuwa da ita.
— Ba magani ko riga-kafin Coronavirus. Har yanzu kuwa, ko da yake ana ta bincike. Amma akwai allurar riga-kafin kamuwa da mura.
An tsakuro wannan bayani ne daga mujallar MIT Technology Review.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari