Mal. Isyaku Garba Zuru, Mawallafin shafin Mujallar ISYAKU.COM da SENIORAPOST.COM, wanda ke karkashin SENIORA NEWS ya yi wannan kira ne lokacin da yake jawabi ga wasu matasa da suka kammala samun horo kan aikin jaridar zamani ta amfani da yanar gizo wajen isar da sakonni ga al'umma a ofishinsa.
Isyaku Garba ya ce, " Duk da yake ina biye da ababen da gwamnatin jihar Kebbi ke yi, tare da taro da ta yi dangane da matsalar coronavirus. Amma duk da kokari da gwamnatin jihar Kebbi ke ganin ta yi kan wannan matsalar, ina ganin cewa har yanzu an bar wani gibi babba da ya kamata a ce gwaamnati ta yi amfani da shi".
Ya kara dav cewa " Idan har gwaamnatin jihar Kebbi za ta iya cire miliyoyin kudin jama'ar jihar Kebbi domin ganin an gudanar da bukukuwan Regatta, da bikin kamun Kifi na Argungu, zai zama kan ka'ida idan gwamnati ta ware kudade domin biyan tallace tallace kan fadakar da al'umman jihar Kebbi kan yadda zasu tafiyar da matsalar coronavirus ta hanyar biyan shafukan labari masu zaman kansu a jihar Kebbi, yan soshal midiya masu ingattacen tsari, da admin ma'abuta amfani da zaurukan whatsapp domin isar da sakon ga jama'a ".
"Ba wai kawai ayi amfani da wadannan yara 'yan soshal midiya domin harkar bukatun siyasa ba kawai, yanzu ne ya kamata ofishin mai ba gwamna shawara kan harkar labarai, da kuma mai ba gwamna shawara kana sabbin hanyoyin sadarwa su shawarci gwamnatin jihar Kebbi domin ta amfana da Bloggers, online publishers, social media influencers da whatsapp group admin domin fadakar da jama'a kan coronavirus ganin irin tasiri da wadannan kafofi suke da a rayukan al'umma".
" Tare da hadin guiwa da ma'aikatan lafiya na jihar Kebbi da sauran masu ruwa da tsaki a harkar lafiya a jihar Kebbi, za a iya fitar da tsararren gabatarwa da yan soshal midiya za su iya ci gaba da yadawa akai-akai ga al'umma dangane da coronavirus, ba wai komi dan soshal midiya ya ga dama ya rubuta ba game da coronavirus a jihar Kebbi domin kauce wa haddasa tsoro a zukatan al'umma".
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari