Gwamnan jihar Edo Godwin Obasaki ya killace kanshi bayan kusantar Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari wadanda sakamakon gwaji ya nuna sun kamu da cutar coronavirus.
Wata sanarwa da ta fito daga hannun mai ba Gwamnan shawara kan harkar sadarwa da tsare-tsare Mr Crusoe Osagie ya ce ana gudanar da gwaji kan halin lafiyar Gwamnan.
Osagie ya ce, duk da yake Gwamnan bai nuna wata alamar cutar ba a tattare da shi, amma ya dauki matakin killace kanshi domin kaucewa cudani da wadanda ke iya zuwa domin yin mu'amala da shi.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari