• Labaran yau


  Coronavirus: An rufe makarantu a jihar Kebbi, duba dalili

  An rufe makarantun framare da na gaba da faramare a jihar Kebbi , ciki har da makarantu masu zaman kansu na faramare da sakandare sakamakon umarni da gwamnatin jihar Kebbi ta bayar na rufe makarantun saboda barazanar cutar Coronavirus har tsawon kwana talatin.

  Tun ranar Asabar aka sallami dalibai na makarantun kwana a jihar Kebbi, yayin da ranar Litinin 23/3/2020 aka sallami yan makaranta na jeka ka dawo.

  Mujallar ISYAKU.COM ya samo cewa da safiyar Litinin, aka sallami yan makarantar sakandaren jeka ka dawo na mata zalla Salamatu Hussaini Girls Government Secondary School da ke unguwar Badariya a garin Birnin kebbi.

  Haka zalika, mun samo cewa babu dalibi ko daya a makarantar kwana na yara maza zalla na kwalejin Nagari College da ke Makerar Gandu a Birnin kebbi.

  Hatta makarantu masu zaman kansu, kamar Unique Progressive Primary and Secondary School da ke bayan babban filin wasa na Haliru Abdu da ke garin Birnin kebbi, sun rufe makarantar sakamakon biyayya ga umarnin gwamnatin jiha.


  Tuni dai yara suka fara amfani da wannan dama domin yin wasa a unguwanninsu, lamari da ke haddasa cudani a tsakaninsu, marmakin su kasance a gidajensu wanda shi ne dalili da ya sa gwamnati ta bayar da wannan hutu.

  Rahotun Isyaku Garba Zuru

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

  Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Coronavirus: An rufe makarantu a jihar Kebbi, duba dalili Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama