Atiku: Gwamnan Bauchi ya yi gwaji, ya rufe kansa saboda yiwuwar yada Coronavirus

Rahotun Legit Hausa

Mun ji cewa akwai wadanda su ka hadu da Yaron tsohon mataimakin shugaban kasa, Muhammad Atiku Abubakar, wanda yanzu ya ke dauke da cutar COVID-19. Labari ya zo mana daga Ladan Salihu cewa Mai girma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya na cikin wadanda su ka shiga jirgi guda da Muhammad Atiku Abubakar. Gwamnan da Tawagarsa su na tare da Yaron Atiku Abubakar ne a cikin jirgin daga Garin Legas zuwa babban birnin tarayya Abuja.

Gwamnan ya ce kawo yanzu garau ya ke. Bayan isowar Alhaji Muhammad Atiku gida a Abuja ne aka fara zargin cewa ya na dauke da wannan cuta ta Coronavirus, an kuma tabbatar da haka bayan yi masa gwaji. Shugaban ma’aikatan fadar gidan gwamnan jihar Bauchi, Malam Ladan Salihu ya bayyana cewa babu shakka Bala Mohammed sun hadu da wannan Bawan Allah kwanaki.

Har ila yau, Salihu ya tabbatar da cewa Mai girma gwamnan ya gaisa da Muhammad Atiku Abubakar, kuma sun yi musafaha, watau sun shafa hannun juna a lokacin. Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa za a iya daukar wannan cuta yayin da aka gaisa da maras lafiya. Cutar COVID-19 ta kan dade kafin ta bayyana a jikin mutum.

A halin yanzu dai Sanata Bala Mohammed ya yi gwaji domin tabbatar da halin da ya ke ciki. Sauran Mukarraban gwamnatin jihar su ma duk sun dauki wannan mataki. Kawo yanzu dai ana ta addu’ar ganin cewa sakamakon gwajin ya nuna Gwamnan da Tawagarsa ba su kai ga kamuwa da wannan cuta da ya zagaya kasashen Duniya ba. Tsohon Mai magana da yawun baki da kuma Kwamishinan, ya shaidawa jama’a cewa Gwamna Mohammed ya killace kansa a halin yanzu, bayan aukuwar wannan lamari.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN