Rahotun Legit Hausa
Babu wanda ya kaiwa tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jamiyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yayinda ya halarci wani taron siyasa a Kano ranar Laraba, wani hadimin sirikinsa kuma yaronsa, ya laburta.
Mai magana da yawun dan takaran gwamnan jihar Kano na PDP a zaben 2019, Abba Kabir Yusuf, wanda akafi sani Abba Gida-gida, Malam Ibrahim Adam, ya bayyana haka, Ya ce babu kamshin gaskiya cikin rahoton cewa an kaiwa Kwankwaso hari bayan halartan zama da wakilan uwar jamiyyar PDP kan zabukan shugabannin jamiyyar a Kano.
A jiya an samu rahoton cewa wasu yan daba a Kano sun kai wa ayarin motocin tsohon gwamnan jahar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso hari a ranar Talata, 17 ga watan Maris. An tattaro cewa an lalata akalla motoci uku a ayarin nasa a lokacin faruwar lamarin wanda ya wakana a kusa da wani otel a birnin Kanon.
A Wani jawabi daga Ibrahim Adam, kakakin Abba Kabir Yusuf, dan takarar gwamna a zaben Kano na 2019, ya ce: “jigon ya tsira ba tare da rauni ba.” Adam ya ce: “Yayinda ya ke barin otel din sai wasu yan daba da aka dauko haya suka farma ayarin motocin sanata Kwankwaso Sannan suka lalata motoci uku mallakar wasu yan majalisar dokokinmu.” Ya Kara da cewa: “Amma Alhamdulillah, anyi taron cikin nasara. Basu cimma abunda suka so ba.”
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari