Rahotun Legit Hausa
A yayinda rahotanni suka bayyana cewa an kara samun karuwar mutane a kalla 19 da suka kamu da kwayar cutar corona a kasar Saudiyya, shugaban masallatan Haramain da ke birnin Makkah da Madinah, Sheikh Sudais, ya bayar da umarnin a nade shinfidun da ke cikin masallatan.
A wata sanarwa da shafin masallatan ya fitar a shafinsa na dandalin sada zumuntar 'facebook' (Haramain Sharifain), an bayyana cewa za an maye gurbin kafet din masallatan da wasu layuka da aka zana a kan tayil din masallatan.
A sanarwar da aka wallafa a shafin, an ga hotunan wasu ma'aikatan masallatan na nade kafet din tare da zana sabbin layukan.
Nade shimfidun masallatan na daga cikin matakan kiyaye wa da kare yaduwar kwayar cutar coronavirus da ke cigaba da yaduwa a sassan duniya.
A cikin makon jiya ne hukumomin kasarSaudiyya suka sanar da rufe masallatan Harami da dakatar da aikin Umrah sakamakon bular annobar kwayar cutar corona.
DAGA ISYAKU.COMLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Tags:
LABARI