Yaki da ta'addanci: NAF ta kaddamar tare da yin gwajin sabon jirgin yaki (Hotuna)

Rahotun Legit Hausa
A kokarinta na cigaba da yaki da aiyukan ta'addanci da sauran kalubalen tsaro a fadin kasa, rundunar sojin sama (NAF) ta inganta tare da kaddamar da wani jirgin yaki bayan an sake duba lafiyarsa da kara masa karfi.
An kaddamar da jirgin yakin (Alpha Jet), NAF 455, a ranar Asabar 21 ga watan Maris, a wani sansanin atisaye na NAF (407 ACTG) da ke Kainji, kamar yadda Air Commodore Ibikunle Daramola, darektan hulda da jama'a ya sanar a jawabin da ya fitar ranar Asabar da yamma.
Bayan kaddamar da jirgin da aka inganta sassansa, an yi gwaji na musamman domin tabbatar da aikinsa.
Kazalika, an kaddamar da wata hanya mai nisan kilomita 2.8 da aka gina domin sada filin atisaye da dakin kwararrun jami'ai na musamman a sansanin na Kainji.
A jawabin da ya gabatar a wurin taron, shugaban rundunar NAF, Air Marshal Sadique Abubakar, ya bayyana gamsuwa da jin dadinsa a kan inganta jirgin yakin, tare da bayyana cewa hakan zai taimaka a yakin da rundunar ke yi da 'yan ta'adda da sauran batagari.
Ya kara da cewa inganta aikin jirgin yaki a cikin gida Najeriya ya bawa NAF damar tsimin kudade masu yawa idan aka kwatanta kudin da za a kashe idan a kasar waje za a yi aikin.
Kazalika, ya bayyana cewa yin aikin a cikin gida zai bawa kwararrun injiniyoyin NAF damar samu kara kware wa a aiki da kuma nunawa duniya irin basirar da suke da ita.
Air Marshal Abubakar ya lashi takobin cigaba da gudanar manyan aiyuka a sansanin na Kainji.
Shugaban rundunar ta NAF ya mika godiyarsa ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a kan goyon baya da gudunmawar da yake bawa bangaren tsaro.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN