Type Here to Get Search Results !

Main event

Covid-19: Jigawa ta rufe iyakakokin ta da Bauchi, Kano da wasu jihohi biyu

Rahotun Legit Hausa

Gwamnatin jihar Jigawa, a ranar Alhamis ta sanar da cewa ta rufe iyakokin ta na kasa da jihar Bauchi da ta ke makwabtaka da ita da wasu jihohin bayan an samu bullar cutar da coronavirus a jihar.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Abba Zakari ne ya shaidawa manema labarai hakan inda ya ce dokar za ta fara aiki daga ranar Juma'a 27 ga watan Maris. Mista Zakari ya ce jihar ta tuntubi dukkan masu ruwa da tsaki a fanin da suka hada da kungiyar direbobi na kasa (NURTW) domin tabbatar da cewa kowa ya bi dokar. Mista Zakari ya ce,

 "Daukan wannan matakin ya zama dole duba da yadda annobar ke yaduwa, tuni jihar Kano ta rufe iyakokin ta da wasu jihohi saboda haka ya zama dole Jigawa ita ma ta yi hakan." Mista Zakari wanda shine shugaban kwamitin ta baci da aka kafa domin kare yaduwar Covid-19 a jihar ya ce sauran hanyoyin da aka rufe sun hada da hanyar da ta hada Jigawa da Kano,

Yobe da Katsina. Kwamishinan ya sake jadadda cewa jihar ba za ta amince da taro na mutane da ya dara 20 ba kuma hukumomin tsaro za su sanya ido domin ganin an bi dokan. Jami'in ya kuma ce, "Duk da cewa a halin yanzu ba samu bullar cutar a jihar ba, ba za mu so mu ga wani daga cikin mutanen jihar mu ya kamu da cutar ba."

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies