• Labaran yau


  Budurwa dauke da tsohon ciki ta sha guba bayan ta gano cewa saurayinta yana da aure

  Rahotun Legit Hausa
  A ranar Alhamis dinnan ne wata budurwa mai shekaru 20 daga jihar Anambra tayi kokarin kashe kanta bayan ta gano cewa saurayinta yana da aure
  Budurwar ana zargin ta sha guba ne domin ta kashe kanta kowa ma ya huta.
  Budurwar da aka bayyana sunanta da Oluchi daga garin Obosi dake cikin karamar hukumar Idemili cikin jihar ta Anambra.
  Rahotanni sun bayyana cewa an ceto rayuwarta sannan kuma 'yan sanda suka kama ta da zargin kokarin kashe kanta.
  Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya tabbatar da faruwar lamarin.
  Ya ce: "A ranar 19 ga watan 3 shekarar 2020 da misalin karfe 4 na yamma, an kai rahoto ofishin 'yan sanda na Awada cewa wata budurwa mai karancin shekaru da aka bayyana sunanta da Oluchi Akabilo ta sha guba da niyyar kashe kanta.
  "Budurwar ana zargin tana da ciki da saurayin nata mai suna Chinedu wanda ba a san ainahin sunan mahaifinsa ba, an bayyana cewa yana da aure har da 'ya'ya.
  "Hankalinta yayi matukar tashi bayan ta gano cewa yana da aure, inda taje ta sayo guba da kudin da saurayin ya bata naira dubu goma domin ta zubar da cikin da ta dauka.
  "An garzaya da ita asibiti mafi kusa dake garin Onitsha, inda 'yan sanda suka kai ta kuma likitoci suka yi iya bakin kokarinsu domin su ceto rayuwarta.
  Jami'in hulda da jama'a na hukumar ya kara da cewa: "Yanzu haka muna cigaba da gabatar da bincike akan lamarin, kuma mun sanya jami'anmu su nemo duk inda saurayin ya shiga, domin tabbatar da ainahin abinda ya faru."
  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

  Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Budurwa dauke da tsohon ciki ta sha guba bayan ta gano cewa saurayinta yana da aure Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama