Rahotun Jaridar Aminiya
An dage daurin auren matashin nan dan jihar Kano Isa Sulaiman da
masoyiyarsa baturiyar Amurka Jeanine Sanchez wanda a baya aka shirya yi a
watan da muke ciki bayan da ta ziyarce shi a gidansu da ke Fanshekara a
watan Janairun da ya gabata.
Mahaifin matashin Malam Sulaiman Isa ne ya shaidawa Aminiya hakan, ta
wayar salula inda ya ce an dage daurin aure, ba a kuma sake sanya rana
ba sai zuwa lokacin da baturiyar zata samar masa
takardun izinin zama
Æ™asar Amurka, ya ce dage daurin auren ya biyo bayan matakin hana wa ‘yan
Najeriya biza da kasar Amurka ta dauka.
Sulaiman, mai shekaru 25 wanda ke karatu a jami’ar Bayero ta Kano ya
shirya auren masoyiyarsa baturiyar Amurka mai ‘ya’ya biyu bayan sun hadu
da ita a kafar sada zumunta ta instagram kimanin shekara guda da ta
shude inda ya yi niyyar ci gaba da karatunsa a Amurka bayan an daura
auren nasu.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari