Abin
mamaki baya karewa a wannan Duniya ta Allah, domin a kullum mukan tashi
ne da jin labarin ababe kala-kala. Wannan labarin wata mata ce mai
suna Mrs. Veronica Iorshe yar shekara 47 daga Mazabar Ugee ta dau cikin
gaba da fatiha bayan dan cikinta da ta haifa ya yi ta aikata lalata da
ita har tsawon wata biyu.
Wannan lamari ya faru a Aliade na karamar hukumar Gwer ta gabas a jihar Benue.
Maigidanta
Sebastian Iorshe, dan shekara 44 ya aureta ne yan shekaru da suka
gabata, amma sai ya kasance Allah bai basu haihuwa ba. Amma kafin
aurensu, dukanninsu sun taba yin aure, kuma maigidanta na yanzu ya rasa
matarsa ta farko sakamakon rashin lafiya. Ita kuma ta rasa mijinta bayan
wani hadarin mota, amma suna da 'da guda daya daga mijinta na farko.
Bayan
tsawon lokaci da aurenta, kuma basu sami 'da ba da mijinta na biyu, sai
yanuwan miji suka fara tsangwamarta, musamman mahaifiyar mijin, wacce
ta ke zargin cewa tana amfani da dukiyar danta watau mijinta domin ta yi
dawainiyar danta da ta zo da shi gidan.
Lamari
fa ya yi zafi har mahaifiyar miji ta zo ta tare a gidan danta watau
mijin matar, sakamakon haka lamaurra suka kara jagulewa matar. Ganin
haka ke da wuya, kuma tana matukar son mijinta, ta lallabe shi domin ya
je ya yi gwajin maniyi amma sai ya ki.
Bayan tsananin
matsin lamba a kan rashin haihuwa, sai matar ta lallabi dan cikinta da
ta haifa da mijinta na farko watau Simon ya yi lalata da ita har tsawon
wata biyu. Sakamakon haka ta dau ciki.
Amma bayan ta
shida wa mijinta cewa tana dauke da juna biyu, sai ya ce alam baram shi
fa wannan ciki ba nashi bane. Sakamakon haka suka dunguma zuwa wani
Asibiti inda aka yi masu gwaji gaba daya wanda ya tabbatar cewa wannan
ciki ba nashi bane domin kwayoyin maniyinsa basu da yawa da zasu iya yi
wa mace ciki.
Daga karshe dai asiri ya tonu, kuma maigida ya koreta daga gidansa.
Daga Isyaku Garba, Muhammed Sani da Nura Kabiru.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari