Wasu bayanan sirri da suka bayyana sun zayyana zargi da ake
yiwa Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle da yin barazana ga
Shuwagabannin kananan hukumomin guda 14 na jam'iyar APC kan sauke kowane
daga cikin su wanda bai sauya sheka zuwa jam'iyar gwamna ta PDP ba.
Wannan zargi da ake yiwa Gwamna Matawalle ya tafi akan
cewar Gwamna Matawalle ya yi dukkan barazana akan
shuwagabannin kananan hukumomin na jihar zamfara wanda duk suke biyayya
ga jam'iyar APC da cewar, duk wanda be aminta da sauya sheka zuwa
jam'iyar PDP ba akwai shirin dauko masa lamarin shari'un zaben da kuma
gabatardashi a gaban yan majalisar dokokin na jihar zamfara don amsa
tambayoyi.
Hakazalika, bayanin na zargi da ake yiwa Gwamna
Matawalle, ya nuna cewa Gwamna Matawalle ya sha alwashin kyale duk wani
Shugaban karamar hukuma wanda ya canja sheka
zuwa PDP a saman kujerar sa ta Shugaban karamar hukuma.
"Yana da kyau dai mu tuna cewar wadannan shuwagabannin
kananan hukumomi 14 na jam'iyar APC an zabe su ne akan dokar zabe ta
kasa, da kuma dukkan dokokin da akebi wajen zaben kowane shugaba na
karamar hukuma don haka zargin yunkurin sauke su da Gwamna Matawalle
yake ba adalci ba ne kuma saba dokar kasa ne" inji wani Musa Gusau..
Matasa Masu Kishin Jihar Zamfara.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari