• Labaran yau


  Kungiyoyin arewa sun kafa rundunar tsaro "Shege-ka-fasa" bayan kafa Amotekun a kudu

  Hadaddiyar kungiyoyin Arewa The Coalition of Northern Groups (CNG), ranar Laraba, ta kafa wata kungiyar tsaro na Arewa da ta rattaba wa suna "Shege-ka-fasa".

  Wannan ya zo ne lokacin da ake ta takaddama kan rundunar tsaro da Gwamnonin kudancin Najeriya suka kafa mai suna "Operation Amotekun" wanda ya ja cece kuce a tsakkanin yan Najeriya.
  Kakakin kungiyar hadaddun kungiyoyin Arewa Abdulazeez Suleiman, ya ce sun samar da rundunar ne domin samar da tsaron kare kai daga karuwar barazanar rashin tsaro a yankin da hakan ya fi kamari, watau Arewacin Najeriya, Duba da yadda wasu mutane daga wani sashe na kasarnan suka kafa tasu rundunar tsaro duk da yake barazanar tsaronsu bai kai na Arewa ba.


  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kungiyoyin arewa sun kafa rundunar tsaro "Shege-ka-fasa" bayan kafa Amotekun a kudu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama