Yanzunnan: Mutum 5 sun mutu wajen hakar ma'adinai a Kano, duba sunayensu

Rahotun Legit Hausa

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane biyar cikin shida da kasa ya ruftawa a Ramin Farar Kasa a kauyen Dauni a karamar hukumar Minjibir na jihar. Mai magana da yawun hukumar, Alhaji Saidu Muhammad ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a a Kano.

Ya ce, "Wani Malam Danlami Murtala kira mu da rana a ranar Alhamis mislain karfe 2.45 na rana daga kauyen Dauni inda ya ce kasa ya ruftawa wasu mutane shida da ke hakar kasa. "Mun aike da jami'an mu nan take bayan an sanar da mu domin su yi kokarin ceto wadanda abin ya shafa amma wani karamin yaro mai shekaru hudu ne kawai aka samu da rai."

Ya bayar da sunan wadanda suka mutu kama haka; Ibrahim Shu’aibu, dan shekara hudu; Dije Shu’aibu, dan shekara 8; Hadiza Shu’aibu, 'yar shekara 12; Nana Idris, 'yar shekara 12; Wasila Nuhu, yar shekara 13; da Sa’ida Lawwali, yar shekara 32.

Muhammad ya ce an mika wa dagajin kauyen, Alhaji Bello Rabi'u gawarwakin wadanda suka rasu inda ya kara da cewa wanda ya yi rai ya samu karaya. Ya shawarci wadanda ke sana'ar hakar kasa ko kuma ma'adinai su rika kulawa sosai wurin yin ayyukansu domin kiyaye lafiyarsu da rayyukansu kamar yadda kamfanin dillancin labarai, NAN, ta ruwaito.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN