PM Express ta ruwaito cewa lamarin ya faru a unguwar Alhaji Afeez Gbadomosi da ke yankin Ejigbo a birnin Ikko,watau Lagos.
Hakazalika, rahotun ya ce Maichael bai bar yar'uwarshi mai suna Mary ba, domin ita ma ya caka mata wuka, kuma yanzu haka tana wani Asibiti inda take jinya rai hannun Allah.
Makwabta sun ce uwayen Michael sun sha wuya a kansa, domin dai sun sha kai shi Jami'a na kudi masu zaman kansu domin ya yi karatu, amma karshen lamari shi ne ana koroshi daga Jami'an saboda rashin kokari, sakamakon harka da kwayoyi da kayan maye.
![]() |
Gidan Barista Clement inda Michael ya kashe uwayensa |
Bayanai sun ce Michael, sanye da gajeren wandon Boxer, ya gidu daga gida, bayan ya kashe iyayensa tare da raunata yar uwarshi da wuka. Sai dai tuni yansanda suka shiga farautar Michael.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari