Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba 2019 yayin da yake ganawa da manema labaru a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja. Legit.ng ta ruwaito cewa Garba Shehu wanda yana daga cikin tawagar shugaba Buhari da ta wuce kasar Rasha domin halartar kasashen Afirka da kasar Rasha da zai gudana a birnin Sochi, ya bayyana cewa shugaba Buhari zai tattauna da shugaban Rasha Viladmir Putin domin sayo ma Najeriya sabbin jirage yaki daga kasar.
"Rasha ta kasance abokiya ga Najeriya dake bamu gudunmuwa ta bangaren Soji wajen yaki da yan ta’addan duk da cewa ba wai mun sanyasu cikin maganan yadda ya kamata bane. Don haka wannan ziyara zata bayar da damar daya kamata ga shuwagabannin kasashe biyu su zauna su tattauna musamman game da batun sayan makamai da jiragen yaki.
” Inji shi. Malam Garba ya kara da cewa nan gaba kadan gwamnati za ta bayyana cikakken bayani game da da cinikayyar makaman, sa’annan ya cigaba da cewa kokarin da Najeriya a baya don sayen jiragen yakin daga Rasha ya samu tasgaro ne sakamakon takunkumi da kasar Amurka ta sanya wa Rashan.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari