Kakakin Majalisar wakilan Amurka Pelosi ta yaga takardan jawabin Trump a wajen taro

Bayan shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya ki gaisawa da Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi, lokacin da ta mika masa hannu domin yin musabaha a wajen taron yanayi da harkokin da kasar Amurka ke ciki, Pelosi ta yaga kofi na jawabin da Trump ya karanta a zauren taron.

Bayan Trump ya gama karanta jawabinsa, yan Majalisa sun mike tsaye domin yin tafi, sai Pelosi ta tashi ta dauki kofi da aka bata na jawabin da Trump ya karanta a wajen taron, sai ta yaga shi yayin da take tsaye a bayan Trum, daga bisani ta dora yagaggen takardar a kan teburi.

Sai daia wani hadimin Trump, kuma mai bashi shawara na musamman, ya ce Trump ya yi babban kuskure, ta hanyar rasa dama ta dinke baraka da ya jawo rarraba tsakanin jama'ar kasar Amurka, sakamakon kin yin musabaha da Pelosi wacce yar jam'iyar Demokrat ce mai adawa da jam'iyar Ripublikan na shugaba Trump mai mulki.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN