Rahotun Legit Hausa
Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa almundahana, EFCC, ta damke kwamishinan aiyuka na musamman na jihar Kano, Mukhtar Ishaq a kan zarginsa da damfara.
A wata takardar da mai magana da yawun hukumar EFCC din ya fitar a ranar Juma’a, Tony Orilade, ya ce an kama kwamishinan a kan zarginsa da ake da waskar da wasu kudade da aka ware na babban birnin jihar Kano din a yayin da yake shugaban karamar hukumar KMC din.
A wani korafi da aka kai a yayin da yake shugaban karamar hukumar KMC din, an zargesa da waskar da N76,000,000 wanda aka ware don aiyukan ci gaba da tallafawa jama’ar yankin. Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, a yayin da yake shugaban karamar hukumar, ya bada umarnin zabtare har N30,000 daga kudin kowacce gunduma ba tare da wani gamsasshen bayani ba.
“Ana zargin kwamishinan da waskar da kadarorin makarantar firamare ta kofar Nasarawa da ke Kano zuwa shaguna, kuma ya siyar da kowanne a naira miliyan goma. Ya kuma waskar da kudaden zuwa amfanin kansa,” EFCC ta ce. Takardar ta kara da cewa za a gurfanar da Ishaq a gaban kuliya nan ba dadewa in an gama bincike.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari