Kashe mazansu: Kotu ta yanke wa Rashida hukuncin kisa a Kano, Maryam Sanda ta kalubalanci hukuncin kisa

Rahotun Legit Hausa

Wata babbar kotun jihar Kano a ranar Jumaa ta yankewa wata mata mai suna Rashida Saidu hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin kisan mijinta, Adammu Ali, ta hanyar turoshi daga gidan tsauni a jihar. An shigar da Rashida kara kotu ne a shekarar 2019 kan zargin ta nada hannu cikin kisar mijinta wanda ya kasance ma’aikaci a kwalejin ilimin tarayya FCE Kano.

Lauyan gwamna, Mariam Jibrin, ta bayyana kotu cewa Rashida ta samu sabani da mijinta ne a gidansu dake unguwar Dorayi kimanin shekara daya da ta gabata. Ta kara da cewa yayinda suka fara fada, sai ta turoshi kasa daga gidan tsauni kuma hakan yayi sanadiyar mutuwarsa.

Yayinda ake shari’ar, an gabatar da shaidu hudu a kotun domin bayar da shaida kan tuhumar da ake mata. Amma Rashida ta bakin lauyanta, Iliya Dauda, ta musanta zargin kuma ya gabatar da nata shaidun.

A bangare guda, Maryam Sanda ta bayyana rashin amincewarta da hukuncin kisan da babbar kotun tarayya Abuja ta yanke mata kuma ta daukaka kara zuwa kotun daukaka kara dake Abuja.

A ranar 27 ga watan Janairu ne mai sharia Yusuf Halilu ya yanke ma Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ya kamata da laifin kashe mijinta Bilyaminu Muhammad Bello, sai dai Maryam ta bayyana hukuncin a matsayin wanda ke cike da son kai da rashin adalci.

Maryam ta ce kotun ta hanata daman sauraronta, sa’annan ta yanke mata hukunci a kan wasu hujjoji marasa kwari duk da cewa shaidun da aka gabatar basu da tabbaci, kuma babu wanda ya bayyana makamin da ake zargin ta yi amfani da shi, balle kuma rahoton binciken gawa da zai tabbatar da abin da ya kashe mijin nata.

Cikin karar da ta daukaka, Maryam Sanda ta hannun lauyoyinta Rickey Tarfa, SAN, Olusegun Jolaawo, SAN, Regina Okotie-Eboh da Beatrice Tarfa ta bayyana hukuncin babbar kotun a matsayin barin sharia, sa’annan ta yi zargin Alkalin bai bata daman bayar da jawabinta ba.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN