Yadda wata mata ta yi wa mijinta mugun duka saboda ya kasa yi mata ciki

An gurfanar da wata matar aure yar shekara 32 mai suna  Mrs. Chinwendu Chita a gaban wani Kotun Majistare da ke Ejigbo a birnin Lagos, saboda ta yi wa mijinta mai suna Okechukwu Chita dukan tsiya, a gidansu da ke titin Alhaji Agbeke, da ke Ago-Okota, a unguwar Isolo, bisa dalilin cewa mijinta ya kasa yi mata ciki

Chiwendu ta ce, an daura masu aure tare da mijinta yan shekaru da suka gabata, amma mijinta ya kasa yi mata ciki, balle su sami da ko diya, ta ce duk da haka mijinta bai damu ba.

Mujallar ISYAKU.COM, ya gano cewa Chiwendu, ta dade tana gana wa mijinta ukuba, ta hanyar dukansa a gida. Mun samo cewa tun 2018, mijinta ya shiga tsoron komawa gida saboda tsananin fitinar matarsa Chiwendu.Rahotanni sun ce, hatta dansanda da ke fadar Ago, ya sha yin sulhu tsakanin ma'auratan, amma lamarin ya gagara.

Hakazalika mun samo cewa matar ta kulle mijinta a daki, ta dinga dukansa da kuyafan miya a fuska, ranar 22 ga watan Disamba 2019, lamari da ya haifar masa da raunuka a fuska.


Majiyarmu ta kara da cewa, Chiwendu, ta tilasta mijinta ya bata N650.000 kafin ta daina dukansa da kuyafar diban miya.


Bayanai sun ce Okechukwu, wanda dan asalin jihar Anambra ne, ya auri Chiwendu daga jihar Abia, duk da yake Okechukwu dan kasuwa ne mai wadata, amma har yanzu basu sami haihuwa da tare da Chiwendu ba. Wannan ne dalili da ya fusata Chiwendu game da mijinta Okechukwu.


Ranar Litinin da ya gabata, Chiwendu ta cakume Okechukwu, ta rungume shi daram, kana ta yi masa dan karen duka. Bayan Okechukwu ya kubuta daga hannunta, sai ya ruga da gudu ya je ya kai karanta wajen yansanda a ofishin yansanda da ke Ago.

Daga bisani an tura wata yarsanda tare da Okechukwu domin ta gayyaci Chiwendu, domin ta je ofishin yansanda, saboda Okechukwu ya yi kararta. Amma sai Chiwendu ta kama yarsanda ta yi mata duka.


Daga karshe yansanda sun yi gangami suka kama Chiwendu, suka gurfanar da ita a gaban Kotu, sai dai bata amsa laifinta ba, sakamakon haka Alkalin Kot ya bayar da belinta a kan N700,000, daga bisani aka tasa keyarta zuwa Kurkuku kafin ta cika ka'idodin beli.


Kotu za ta ci gaba da sauraron shari'ar ranar 11 ga waatan Maris 2020.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN