Rahotun Legit Hausa
Jami’an ‘yan sandan kasar Amurka na farin kaya sun kama wani mutum mai shekaru 25 mai suna Roger Hedgpeth. Roger dai dan asalin Brandon ne na Florida kuma an kama shi ne da wuka wacce ya dauka da niyyar kashe shugaban kasa Donald Trump.
Jaridar Dailymail ta ruwaito cewa ‘yan sandan sun kama mutumin ne a farfajiyar fadar shugaban kasar Amurkan wacce aka kira da “White House” a ranar Asabar, 8 ga watan Fabrairu. Kamar yadda ‘yan sandan sashen suka sanar, Hedgpeth ya amsa lafinsa inda ya tabbatar da cewa kisan kai yaje yi da wukar.
Bayan kwace wukar da aka yi, jami’an sun ce an tsare shi tare da fara bashi kulawa da dubawa ga kwakwalwarsa. Rahotanni sun bayyana cewa, Hedgpeth dai da aka kama da Pistol ya gudo ne daga wani gidan mahaukata.
A wani rahoto na daban, an ji cewa Trump ya kori manyan jami’ai biyu wadanda suka bada shaida don tumbuke shi daga kujerarsa.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari