An kashe wani jigo a jam'iyar APC


Rahotun Legit Hausa

Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta tabbatar da kama wani mai hada magani da ma'aikatansa a kan zargin yi wa wani mutum dukan mutuwa a Owerri. Mai magana da yawun rundunar, SP Orlando Ikeokwu, ya ce lamarin ya faru ne a yankin Umuguma da ke birnin Owerri din.

Wakilin jaridar Daily Trust ya gano cewa, mutumin da aka kashe mai suna Damian Ali, jigo ne a jam'iyyar APC. Mai shagon siyar da maganin ne tare da ma'aikatansa suka halaka shi. An gano cewa, Ali dan asalin Nkarahu ne da ke karamar hukumar Ohaji/Egbema da ke jihar Imo.

Yayi yunkurin tsayar da motar shi ne a gaban shagon siyar da magungunan ne wanda hakan ya jawo hayaniya tsakanin shi da mamallakin shagon. Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce an kama mai siyar da maganin tare da ma'aikatansa don amsa tambayoyi.

An kuma tura 'yan sanda daga cikin rundunar don kwantar da tarzoma a yankin. Ya ce da kanshi mai maganin ya kai kanshi gaban 'yan sanda. Kwamishinan 'yan sandan jihar, Olaniyi Fafowora ya bada umarnin aiwatar da gamsasshen bincike a kan lamarin.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari