Duba yadda wasu yansanda suka sha kunya bayan sun kwace wani babur a Lagos

Wasu yansanda sun kwashi kunya a birnin Lagos da sanyin safiyar Alhamis, bayan sun kwace wani babban babur kirar Power Bike daga wajen wani matashi mai suna Nmutaka Chikwenduyayin, da yake kan haryarsa ta zuwa wajen aiki.

ISYAKU.COM ya samo cewa nan take jama'a suka kewaye yansandan, kuma wasu suka tambayesu ko wannan babur shi ma Okada ne ko Achaba da Gwamnati ta hana wanzuwarsu a titunan birnin Lagos.

Duk da roko da tambayoyi da alfarma da jama'a suka nema domin yansandan su sakar wa Nmutaka babur dinsa, amma yansandan sunki sauraron jama'a.

Daga bisani wani bawan Allah ya daga wayarsa ya kira Shelkwatan yansanda a birnin Lagos, kuma nan take aka sa yansandan suka sakar wa Nmutaka wannan babur ba tare da wani jayayya ba.

Wanda haka ya nuna yadda "wa ka sani ko waye kake da" a cikin tsarin jami'an tsaro, da harkokin Gwamnati ke tasiri wajen neman alfarma a kan lamurran rayuwan yan Najeriya

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN