Yadda wani mutum ya yi aman harsashi shekara daya bayan an harbeshi da bindiga a kai

Rahamar Allah baya karewa a Duniyarnan tamu, domin dai wani bawan Allah ne ya yi aman wani harsashi da aka harbeshi da shi shekara daya da ta aagabata.

ISYAKU.COM ya samo cewa wasu yan bindiga ne suka harbeshi a kai, a kusa da gidansa da ke unguwar hanyar Alamieseigha na hanyar Apolo da ke birnin Yenagoa, sakamakon haka aka garzaya da shi zuwa Asibitin tarayya FMC da ke Yenagoa.

Mun samo cewa Likitoci sun ce sai idan raunukan ciwon da ya samu a kai sun warke tsaf kafin a yi masa tiyata domin a cire harsashin daga kansa.

Sai dai wannan bawan Allah ya yi aman wannan harsashi da ya fito daga kansa cikin sauki, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gidan wani abokinsa. Bayan ya isa daidai wajen da aka harbeshi da bindiga a bara, sai ya ji kamar amai, kwatsam sai ya amayo wannan harsashi daga bakinsa.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN