Rahotun Legit Hausa
Wata Tirela dauke da kaya ta murkushe wani jami'in dan sandaranar Laraba har lahira a hanyar Owerri/Okigwe, jihar Imo kan karbar na goro hannun direba.
Hadarin da ya faru a garin Atta, karamar hukumar Ikeduru ta jihar Imo ya tayar da tarzoma.
Ba tare da bata lokaci ba, jami'an yan sanda suka dira wajen inda suka hana mutane matsawa kusa da gawar dake kwance a kasa.
Hakazalika Direban Tirelan ya arce da motarsa a guje.
Wani direba mai suna Iyke Don, ya bayyana manema labarai cewa direban motan ya murkushe dan sandan ne bayan ya tare shi domin karbar N50 na goro.
Ya ce tirelan ta dumfaro a guje kawai ta take da dan sandan saboda ya ki tashi daga hanya.
Yace: "Wata tirela dauke da kaya ta murkushe bayan ya tsareta kuma taki tsayawa. Sauran jami'an yan sandan sun kurewa direban gudu amma ban tunanin sun iya cimmasa."
Da aka tuntubi kakakin hukumar yan sandan jihar, Orlando Ikeokwu, ya tabbatar da labarin.
Yace: "An fada mana. anzu nike ji. Hukumar ta kaddamar da mataki. Abun bai yi mana dadi ba."
A bangare guda, Mazauna Jiddari Polo a babbar birnin Borno, Maiduguri sun bayyana cewa sun ji harbe--harben bindiga da daren nan.
Hakan ya faru ne bayan ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari ya kai gain don jajintawa al'ummar jihar kan kisan mutane 30 a garin Auno ranar Lahadi.
akalla mutane biyar sun jikkata yayinda Boko Haram sukayi kokarin shiga garin.
An tattaro cewa yan ta'addan sun shiga garin Maiduguri ne bayan Sallar Isha ta Addawari, unguwar Jiddari Polo inda suka harba roka da ya jikkata mutane 5.
Wani mazauni, Ali Maji Bukar, ya bayyana cewa na garzaya da wadanda suka raunata Asibitin jihar domin jinya.
"Bamu san abinda ya faru ba. Sai muka fara jin harbe-harbe a bayan gari da kuma hanyar Damboa." Yace
Sanda Bunu, wanda mazaunin Jiddari Polo ne ya ce bai ka yan ta'addan ba amma ya riga harsasai na yawo a sama.
"Jami'an tsaro sun zaburo da wuri kuma suka kawar da yan ta'addan amma har yanzu mutane na bakin hanya." Yace
DAGA ISYAKU.COMLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari