Rahotun Legit Hausa
Taron kungiyoyin Arewa a karkashin lemar NYSC sun fadawa
shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a dalilin rashin tsaro da ake ta fama da shi
yayin da ya ke ofis. NYC ta koka game da kashe-kashen da ake yi a halin yanzu a
Najeriya, wannan ya sa kungiyar ta ce lokaci ya yi da shugaba Buhari zai
tattara kayansa ya bar kujerar mulki.
A cewar kungiyar NYC ta bakin shugabanta na kasa, Muhammad
Ishaq, zai fi dacewa da Muhammadu Buhari ya yi murabus kafin Najeriya ta zama
irin Somaliya. Mista Muhammad Ishaq ya yi wannan jawabi ne a birnin tarayya
Abuja, ya na mai cewa kasar ta koma halin da ta shiga ciki a lokacin da
Goodluck Jonathan ya ke mulki.
Da ya ke magana a Ranar Laraba, Ishaq ya bayyana cewa
sha’anin tsaro ya tabarbare, kuma a kan hakan ne ma aka yi waje da gwamnatin
baya ta jam’iyyar PDP da ta shude. Kungiyar ta nuna cewa shugaban kasa Buhari
ya gaza cika alkawarin da ya yi wa 'Yan Najeriya na cewa zai kawo zaman lafiya
a fadin kasar idan har aka zabe shi.
Ko dai ace halin da ake ciki ya fi na lokacin Jonathan tabarbarewa
ko kuma ace akalla abin ya kai irin abin da ya auku a lokacin gwamnatin shugaba
Goodluck Jonathan. Ganin kura ta kai bango a halin yanzu, Mista Ishaq ya ce:
Lokaci ya yi da ba za a iya cigaba da daukar wani uzuri ba.
“Buhari ya gaza kare rayuka da dukiyoyin al’umma. NYC ta
kare jawabin ta da cewa: “Watakila bai da niyyar yin haka ne, ko kuma ba zai
iyan ba, don haka ya yi murabus, ya ceci kasar nan daga wargajewa gaba daya.”
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari