Kalli yadda gwamnan APC ke shirin karbar mulki kafin kotu ta kwace kujerarsa

Rahotun Legit Hausa
Duniya makwanta rikici, kamar yadda masu iya magana suke fadi, wani sabon gwamnan jam’iyyar APC dake jiran gado a jahar Bayelsa ya ga rashi ya ga samu, yayin da kotun koli ta tsige shi ana gobe bikin rantsar da shi.
A ranar Alhamis, 13 ga watan Feburairu ne kotun kolin Najeriya ta soke nasarar da dan takarar gwamnan jahar Bayelsa a jam’iyyar APC ya samu, David Lyon tare da mataimakinsa Biobarakuma Degi-Eremioyo.
Ta leko ta koma: Kalli yadda gwamnan APC ke shirin karbar mulki kafin kotu ta kwace kujerarsa
Gwajin karbar mulki
Sai dai jim kadan kafin samun wannan hukunci, an hangi gwamnan tare da mataimakinsa suna gudanar da shirye shiryen rantsaarwarsu da a da za’a gudanar da shi a ranar Asabar, 15 ga wata, inda gwamnan ya shiga mota tare da jami’an tsaro a filin wasa na jahar yana gwajin yadda taron rantsarwar za ta kasance.
Gwamnan ya yi gwajin shiga motar rantsarwa, ya yi gwajin yadda zai tsaya kikam yayin da Yansanda suke masa faretin ban girma, ya yi gwajin yadda zai zagaya filin a cikin motar rantsarwa har ma yana kujeru bai-bai tare da jinjina da godiya, ashe ashe duk ba zata kai ga haka ba, duniya kenan.
Ta leko ta koma: Kalli yadda gwamnan APC ke shirin karbar mulki kafin kotu ta kwace kujerarsa
Gwajin karbar mulki
Alkalin kotun koli da ya karanta hukuncin da kotun ta yanke, mai sharia Ejembi Ekwo ya bayyana cewa kotun ta soke nasara Lyon ne sakamakon mataimakinsa Biobarakuma ya mika ma hukumar INEC takardun bogi gabanin tsayawa takara a zaben daya gudana a ranar 16 ga watan Nuwamba.
PDP ce ta shigar da karar dan takarar mataimakin gwamnan gaban kotun, don haka kotun ta bayyana cewa tun da har ya gabatar da takardun bogi ga INEC, toh rashin gaskiyarsa ta shafi nasarar maigidansa gaba daya, saboda haka ta haramta zaben da suka ci gaba daya.
Dama a ranar 12 ga watan Nuwambar 2019 wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta haramta ma Degi takara, amma sai ya daukaka kara. Daga karshe Alkalin ya umarci INEC ta mika takardar nasara ga dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP, kuma ta bada umarnin a rantsar da shi a ranar Asabar, 15 ga wata.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN