Isyaku Garba Zuru
Kimanin baligai maza guda 10,000 suka taru domin gudanar da shagulgulan "Tsiraici" a garin Okayama na kasar Japan, domin aiwatar da bikin "Hadaka Matsuri" wanda biki ne mai hadarin gaske da ake gudanarwa a ranar Asabar na karshen kowane watan Fabrairu a shekara. An gudanar da bikin na bana a wajen bauta na Saidaji Kannonin a kasar Japan.
Kimanin mutum 10.000 sanye da wani bantai da ake kira "Fundoshi" da fararen safan kafa da ake kira "Tabi" sun yi ta zagayawa wajen bikin da ake gudanarwa domin nuna farin ciki bisa samun amfanin gona mai kyau, nassara da zama cikakken mutum, biki da ake gudanarwa a cikin yanayi da ruwa mai tsananin sanyi.
Bayan sun gudanar da ka'idan al'ada, sai mutanen suka taru a ginin Mujami'ar bauta da misalin karfe 10 na dare agogon kasar Japan, kuma aka kashe wutan fitilu. Daga bisani wani shehin Malaminsu ya jefa bandir 100 da wasu kananan itatuwan al'ada da "Shangi" na samun sa'a guda 20 cikin mutanen, daga tagar gini mai tsawon mita 4 daga tsawon kansu.
An camfa cewa duk wanda ya sami cafke daya daga cikin sanda ko "Shangi" zai kasance cikin rayuwa mai cike da sa'a, nassara, tare da samun dukiya a wannan shekara.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari