Ya yi mata hidima ta kare Jami'a: Saurayi ya kashe kanshi domin budurwarsa za ta auri wani

Wani matashi mai suna Mr. Ossy dan asalin garin Aguleri a jihar Anambra, ya rataye kanshi a bishiyar Mangoro da igiya har ya mutu.

Ganau ba jiyau ba, wani mai suna Ahamefule Bright, ya ce, Ossy ya kashe kanshi ne bayan ya sami sakon cewa budurwarsa mai suna Miss Melisa Nnaji, yar asalin jihar Enugu, da ya dauki nauyin karatunta har ta kammala Jami'a, za a daura mata aure da wani mutum.

Mujallar ISYAKU.COM ya samo cewa, Ossey da Melisa sun yi alkawarin cewa za su yi aure idan ta kammala karatun Jami'a, sakamakon haka Ossy ya dauki nauyin karatunta har ta kammala, amma sai ta juya masa baya za ta auri wani.

An sa ranar daura wa Melisa aure ranar 18 ga watan Maris 2020, kafin mutuwar Ossy.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN