Rahotanni sun ce, dan sandan mai suna ASP Christopher Akpan, wanda ke sashen FSARS, ya fadi ne a cikin ban dakin ofis, bayan dawowarsa daga wajen wani aiki da suka yi ranar Juma'a.
Bayan sun dawo daga wajen aikin ne, sai ASP Akpan ya shiga ban daki, amma daga bisani sai ya yanke jiki ya fadi.
An garzaya zuwa Asibiti da ASP Akpan, amma sai Likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Dan asalin jihar Akwa Ibom , ASP Akpan ya mutu ya bar matarsa da yara.
Kafin mutuwarsa, Akpan yana zaune a Barikin yansanda da ke Okota a birnin Legas.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari