AGF: Abubuwan more rayuwa za a gina da kudin satar Abacha da aka dawo da su

Rahotun Legit Hausa

Ministan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin Najeriya, Abubakar Malami SAN, ya ce aiki za a yi wa ‘Yan kasa da kudin satar Sani Abacha da aka dawo da shi. Abubakar Malami ya yi wannan jawabi ne ta bakin Hadimin da ke taimaka masa wajen hulda da jama’a, Dr. Umar Gwandu, inda ya musanya rahotannin da ke yawo.

Ministan ya bayyanawa Manema labarai cewa sam babu wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnan jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu ko ma wani. Malami ya nuna rade-radin da aka ji na cewa Najeriya za ta ba wani Mutum dala miliyan 100 daga cikin kudin satar Sani Abacha da aka karbo daga hannun kasar Amurka.

A cewar Ministan, Atiku Bagudu ya na kara a kasar Amurka inda ya ke neman hakkinsa a cikin kudin da ake zargin Marigayi Sani Abacha da sacewa daga asusun Najeriya. Ana zargin Bagudu, wanda ya na cikin manyan jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, da hannu a badakalar Abacha, wanda hakan ya kai shi ga zama a gidan yari a Amurka.

Malami SAN ya ce gwamnatin Buhari ta na kokarin karbo dukiyar da James Ibori da Deziani Alison-Madueke su ka sace daga asusun kasa a lokacin da su ke mulki. Har ila yau, Ministan kasar ya bayyana cewa za ayi amfani da wannan kudi wajen aikin hanyar Abuja zuwa Kano, da gadar Neja da kuma titin Legas zuwa Garin Ibadan.

 “Babu wani mutum da aka yi da shi cewa za a ba shi kaso daga cikin wannan kudi a takardun da aka tattauna a kansu a majalisar zartarwar tarayya.” Inji Hadimin Ministan.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN