Wani mutum da har yanzu ba a gane ko waye ba, ya mutu a dakin wani Otel a kudu bayan ya kwana tare da wata budurwa mai suna Precious yar asalin jihar Akwa-Ibom. An sami wasu magunguna a jakar mamacin tare da wani magani mai kama da na kara kuzarin maza wajen jima'i.
ISYAKU.COM ya samo cewa Precious ta hadu da wannan mutum ne bayan kawarta ta gaya mata cewa, shi mamacin ya dawo ne, kuma yana neman yarinyar da zai kwana da ita.
Precious ta ce " Bayan mun hadu da wannan mutum, sai muka daidaita tsakaninmu, daga bisani muka je muka ci abinci tare, sai muka je muka kwanta muka yi barci. Da misalin karfe biyar na safe, sai ya tayar da ni kuma muka sadu, daga bisani muka koma muka kwanta. Bayan misalin awa daya, sai na shirya domin in tafi. Na tayar da shi amma bai tashi ba, na yi ta tayar da shi amma bai tashi ba, daga nan ne na je na gaya wa mutanen da ke aiki a Otel da muka kwana".
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari