Wani tsohon dan majalisar tarayya ya yi wani abin alhairi da ya ba jama'arsa mamaki

Tsohon dan Majalisan tarayya mai wakiltar Birnin kebbi, Kalgo da Bunza a zauren Majalisar Wakilai na tarayya Hon. Dr. Abdullahi Muslim, ya sake ba jama'ar mazabarsa mamaki, bayan ya basu wani tallafin bazata, a ofishinsa da ke unguwar GRA a garin Birnin kebbi ranar Asabar.

Hon. Muslim, ya yi ayyuka guda arba'in da shida (46), a zamanin da ya wakilci jama'ar Mazabarsa na tarayya a Zauren Majalisan tarayya. Ayyuka da har yau jama'a ke ci gaba da more ingancinsu. Hakazalika, tallafi da ya bayar a cikin shirin, yana ci gaba da zama madogaron abin samun na masarufi domin dogaro da kai ga jama'ar Mazabarsa.

Bayan saukansa daga kujerar Majalisan wakilai na tarayya, bayan zabukan 2018, Hon. Abdullahi Muslim, ya gudanar da ayyukan alhairi har guda goma sha biyu (12) a Mazabarsa ta Birnin kebbi , Kalgo da Bunza, duk da yake baya kan kujerar wakilci.


Daga cikin ayyukan da Muuslim ya yi bayan ya sauka daga Kujerar dan Majalisa, har da:

1. Samar da kulawan Likitoci ga marasa lafiya (Free Medical Outreach) inda aka gyara wa masu matsalar idanu tare da samar masu magani, har da Madubai, kuma fiye da mutum dubu biyu (2000) sun amfana da wannan aiki.

2.. Hon Abdullahi Muslim ya raba taki domin noma, duk a wannan wuri dai.

3. Ya ranba tahunan (injimin) nika da na ban ruwan aikin gona ga jama'ar mazabarsa, ya bayar da wadannan kayaki a ofishin koyar da sana'oin hannu na tarayya da ke jihar Kebbi watau National Directorate for Enployment NDE. An bayar da wadannan kayaki wata uku da suka gabata.

4. Ginin Asibitin shan magani a kauyen Junju, wanda an kammala wanda aka kashe naira miliyan ashirin da biyu wajen ginawa..

5. Ginin aji guda uku a makarantar Islamiyya a unguwar Sarakuna, a Makarantar Malam Dan Malam, da teburra da kujeri, har da littafai. An yi wannan aiki wata bakwai da suka gabata.

6. An bayar da tallafi ga jama'ar Mazabansa wata hud da suka gabata a dakin taro na Salamatu Hussaini da ke garin Birnin kebbi wata hudu da suka gabata. An ba maza sittin (60) mata arba'in (40) tallafi.

7. Ya gina fanfunan hannu na ban ruwa, guda uku, daya a hanyar Kola a cikin unguwar Badariya a garin Birnin kebbi, daya a tungar Dole da ke hanyar garin Raha, daya a Masallacin Juma'a da ke bayan Oando a garin Birnin kebbi.

8. Ya yi injimin burtsatse mai amfani da hasken rana mai dauke da tankin ruwa mai yawan lita dubu goma (10,000 ltrs) a shiyar Zabarmawa da ke garin Birnin kebbi.

9. Ginin masaukar baki wanda ake ginawa yanzu haka, kuma zai ci kudi har Naira Miliyan ashirin da uku N23m a garin Raha.

10. Sai kuma ginin dakin taro na kabilar Igbo (Igbo hall) a unguwar Badariya a garin Birnin kebbi.

11.Hon. Muslim ya raba taki buhu dari uku (300), injin ban ruwa guda dari (100) da robar tiyo na ban ruwa da pipe nasu. An bayar da kayakin ne ga maza da mata, yan Mazabar Birnin kebbi, Kalgo da Bunza, wanda Hon. Abdullahi Muslim ya wakilta.

Hon. Abdullahi Muslim, ya gudanar da wadannan ayyuka ne bayan ya sauka daga kujerarsa, lamari da masu fashin baki kan harkokin siyasa a jihar Kebbi, suka alakanta da yanayin gaskiya, tsoron Allah, da dattaku da suka zama hali, akida da al'ada ga Abdullahi Muslim.


Wani dattijo mai suna Malam Nuhu Dan Baiwa, ya shaida wa Mujallar ISYAKU.COM cewa " Gaskiya abin da wannan bawan Allah ke yi, alama ne na neman gamawa lafiya a rayuwarsa. Duba ka gani, baya kan kujerarsa, amma duba yadda yake ta tallafa wa jama'a. Irin wadannan mutane masu amana, mutunci da dattaku muke so a fagen siyasa a jihar Kebbi. Allah ya taimake shi, ya kuma kare shi daga sharrin nasi wal jinni".

Daga cikin wadanda suka halarci wajen rabon kayakin na yau har da Sarkin Sudan na Kalgo Alhaji Haruna Jada, da sauran manyan mutane da jama'ar Mazabar Birnin kebbi, Kalgo da Bunza.
Rahotun Isyaku Garba Zuru

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari