Ma'aikatan gidan mai na Con Oil a unguwar Apapa da ke Lagos, sun kashe wata katuwar mesa da ta boye a cikin ramin dakin duba tayoyi da juyen bakin mai ranar Juma'a.
Wani bawan Allah da ya je domin ya dauko wani abu ne a ramin, sai ya gan macijiyar kuma ya shaida wa jama'a. Lamari da ya sa jama'a suka kawo dauki domin kashe wannan mesa.
Bayan jama'a sun kashe mesan ne, sai aka gano cewa ta riga ta saki kwayakwayi 48 a cikin ramin. Daga bisani jama'a suka kwashe suka je suka dafa, wasu kuma suka soya suka yi kalaci.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari